Shugaba Muhammadu Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin Nijeriya ta bakin babbar mataimakiyar shugaba Buhari ta musamman kan harkokin kasasshen ketare, Abike Dabiri-Erewa ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa dan Nijeriya a kasar Afrika ta kudu.

Misis Dabiri-Erewa ta bayyana takaicin kisan Clement Nwaogu a kasar Afrika ta Kudu a wata sanarwan da ta fitar a Abuja a jiya.

Nwaogu ya gamu da ajalinsa bayan da wasu da ba a san ko su wane ba suka cinna wa motar ‘dan Nijeriyan wuta a birnin Rustenburg da ke kasar inda suka kona shi kurmus.

Wannan kisan dai na zuwa ne kwanaki 10 kacal bayan kashe wani dan Nijeriya daban mai suna Thankgod Okoro mai shekara 30, dan asalin Jahar Enugu.

Kididdigar da aka yi ta nuna cewa izuwa yanzu adadin ‘yan Nijeriya da aka kashe a kasar Afirka ta Kudu a rikicin kyamar baki ta cigaba da kunno kai a kasar ya kai 115 daga watan Fabrairun 2016.

LEAVE A REPLY