Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello

Gwamnatin jiharNeja ta bayyana cewar ta kashe Naira biliyan biyu domin sayawa Malaman Firamare a fadin jihar kekunan hawa da suka kai guda 10,000 domin jin dadin aikinsuna koyarwa.

Kwamishiniyar ilimin jihar Fatima Madugu ce ta bayyana hakan a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a Minna babban birnin jihar.

A cewarta daga cikin kudin Gwamnatin ta samu bashin biliyan biyu daga bankin UBA domin cikawa ta sayawa Malaman Firamaren jihar keken hawa.

Ta karadacewar za’a baiwa kowanne Malamin Firame keken hawa bashi akan zunzurutun kudu Naira 200,000 kowannensu.

 

LEAVE A REPLY