Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta bayyana kudurinta na samar da gidaje 100,000 masu saukin kudi a duk shekara a fadin kasarnan.

Minisatn kasa a ma’aikatar ayyuka da gidaje da makashi Hassan Zarma, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yaje ran-gadin duba ayyukan wasu gidaje a birnin Lafiya na jihar Nasarawa.

Ministan ya bayyana cewar, Gwamnati zata samar da gidajen ne akan Naira miliyan 2 zuwa miliyan 5 masu dakuna daya marasa bene, domin amfanin talakawa masu karamin karfi.

Ya cigaba da cewar a wannan shiri, kananan ma’aikata da suka hada da masu zane zane da direbobi da masu aikin hannu zasu iya mallakar sabbin gidajen da Gwamnatin zata samar a farashi mai rahusa na miliyan 2 zuwa miliyan 5.

Ko me zaku ce kan wannan batu?

LEAVE A REPLY