Adamu Adamu

Ministan Ilimin tarayyar Najeriya, Aamu Adamu, a ranar Litinin ya bayyana cewar Gwamnatin Najeriya ba zata kuma yadda da karatun Digirin da aka yi a wasu jami’o’i na kasashen Benin da Togo da Ghana da kuma Kamaru ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a llokacin da yake kaddamar da wani kwamiti da zai tantance daliban Najeriya 40,000 da suka yi ko suke yin karatun digiri a jami’o’in kasashen waje.

Malam Adamu yace karatun digiri daga wadancan kasashe cike yake da ayar tambaya, dan haka Gwamnati ba zata bayar da aiki da karatun wadancan kasashe ba, haka ma kamfanoni da ‘yan kasuwa.

A cewarsa, bukatar hakan ta taso ne sabpda yadda aka samun bayanai kan shaidar takardun digiri na bogi da ‘yan Najeriya suke samowa a wasu jami’o’i da ba su da inganci.

Malam Adamu Adamu yace,binciken farko da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta gudanar ya nuna cewar a kalla dalibai 40,000 ‘yan Najeriya da suke dauke da takardun shaidar kammala karatun digiri na daya a wasu jami’o’i da yawa na kasashen Afurka bai da inganci.

A saboda haka ne, Ministan ya kafa wani kwamitin mutum 16 da zasu fitarda hanyoyin da za’a dinga bibiyar wannan takardun shaida da ‘yan Najeriya suke samowa a kasashen waje.

Haka kuma, yace Gwamnati zata kafa tsauraran sharudda ga daliban da suke son samun iznin Gwamnati domin zuwa karatu kasashen waje.

 

LEAVE A REPLY