Daga Zaidu Bala

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa zata sanya ido don Kare Rayuwar Giwayen da Sunka bayyana a Karamar Hukumar Mulkin Koko Besse da Bagudo a jihar Kebbi.

Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen. Atiku Bagudu da kansa yayyi Kira ga Al’ummar Kauyukkan da Giwaye sunka bayyana a Yankunansu na cewa kada su taba Giwayen kuma Al’ummar Yankin Sunyi Alkawalin Kare wadannan Giwaye inda Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi yayyi godiya ga Sarakunan yanki da kuma shugabannin Al’ummar yankin akan yadda sunka kare wadannan Giwaye da sunka zo a yankin Karamar Hukumar Mulkin Koko Besse da Bagudo a Jihar Kebbi.

Yanzu haka giwayen na cikin Garin Ganten Tudu da Garin Ganten Fadama duk a cikin Karamar Hukumar Mulki ta Bagudo dake Jihar Kebbi. Inda Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Bagudo da Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kebbi sunka bayyana cewa Al’ummar yankin Sunci yabo da Jinjina akan yadda basu yarda sunka taba wadannan Giwaye ba.

Kuma Manoman yankin Sun bayyana cewa Giwayen nayi musu Barna ga affanin Gona amma duk da haka basu tabasu ba don wannan shine karo na farko da sunka fara ganinsu a cikin yankunansu.

*Mataimakiya ta Musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi akan harakar Sadarwa ta Zamani Hajiya Aisha Augie ta bayyana wannan Labari

LEAVE A REPLY