Gwamnatin jihar Katsina a Arewacin Najeriya, ta bayyana cewar ta kashe zunzurutun kudi naira biliyan 2 domin gina kwalbati a garuruwa goma na jihar a shekarar 2017.

Kwamishinan muhalli na jihar, Hamza Faskari ne ya bayyana hakan a ranar litinin a lokacin da yake magana da manema labarai.

“”Mun ci nasara gina Kwalbati ta zamani, wadda ambaliyar ruwa ba zata iya yin gaba da ita ba a wasu garuruwan jihar Katsina”

“Gwamnatin Katsina ta kashe wannan zunzurutun kudin ne domin kaucewa ambaliyar ruwa a wadannan yankuna da aka gina magudanan ruwa”

“Garuruwan da aka gina wadannan magudanun ruwan sun hada da Funtuwa, Malumfashi, Dutsin-ma, Mani, Kankiya, Musawa, Matazu, Mai’adua da kuma karamar hukumar Daura”

“Haka kuma, Gwamnati ta gina magudanun ruwa masu yawan gaske a cikin birnin Katsina”

“A cikin birnin Katsina, Gwamnati ta gina wadannan kwalbatoci a unguwanni kamar haka: Kofar Kaura, Kofar Kwaya, Gadar-Nayalli, Adeleke, Kofar Marusa da kuma Kofar Sauri”

Haka kuma, an gina karin wasu magudanun ruwan a kofar Soro, da babban asibitin Yammawa da Kofar Sauri da sauransu”

Mista faskari ya kara da cewar, Gwamnati ta ware sama da Naira biliyan 1.8 a kasafin kudi na wannan shekarar domin gina kaarin Lambatu a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina, domin kaucewa ambaiyar ruwa.

Haka kuma, ya jinjinawa Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari sabida yadda ya baiwa harkar muhalli muhimmanci domin itace ke da alaka kai tsaye da rayuwar al’umma.

Sannan kuma, Kwamishinan ya bukaci al’ummar jihar da su cigaba da baiwa Gwamnan jihar goyon baya domin samun tagomashin demokaradiyya.

Ambaliyar ruwa kusan abu na da duk shekara ake fama da shi a jihar Katsina, wanda yake sanadiyar rasa muhalli da asarar rayuka a wasu lokutan.

 

NAN

LEAVE A REPLY