Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu akan wata takarda tare da Bankin duniya domin gina titi mai tsawon kilomita 500 a cikin kauyuka da birane na jihar Kano.

Wannan bayani yana zuwa ne a wata sanarwa da Abba Anwas daraktan yada labarai na Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanar ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda yace za’a gina titi mai tsawon kilomita goma goma a kowacce karamar hukuma dake jihar su 44.

Sanarwar ta kara da cewar,kwamishinan raya karkara da birane na jihar Kano, Musa Kwankwaso, shi ne ya nemi hakan a lokacin da yake wani rangadin tare da Gwamnan Kano a kananan hukumomin jihar 44.

Za’a gina wannan titi ne domin sada kauyuka da birane, da kuma samun damar tafiyar kayan amfanin gonaa ba tare da samun wahala ba.

“Bankin duniya zai sanya idanu kan yadda za’a samu hanyoyin shiga da fita da kayan amfanin gona musamman a yankunan karkara, Gwamnati zata tabbatar anyi abinda ya dace wajen samarwa da mutanan kauye abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da sauransu”

“A yayin wannan aiki, kowacce karamar hukuma a jihar Kano ba zata gaza samun titi mai tsawon kilomita 10 ba”.

Wannan aikin na daga cikin kudurin Gwamnatin Ganduje na ganin ta samarwa da mutanan karkara ayyukan more rayuwa da kuma samun tagomashin romon demokaradiyya”

 

NAN

LEAVE A REPLY