Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamarda yin amfani da duba gari da zasu bi gida gida domin ilmantar da mutane kan kariya daga kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa.

Kwamishinan lafiya na jihar kaduna, Paul Dogo, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai  na Najeriya, NAN, ta samu ranar Lahadi a jihar Kaduna, inda yace, Gwamnati a shirye take ta dakile yaduwar cutar Kwalara da Sankarau da sauran cututtuka masu saurin yaduwa.

Gogo yace, an shirya hakan ne domin kare al’umma daga kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa a jihar.

Ya bayyana cewar, Gwamnatin jihar bata samu labarin bullar wata cuta dake saurin yaduwa ba a kananan hukumomin jihar 23, ta kuma tabbatar da al’umma cewara shirye take da dukkan wata barazana ta wata cuta dake saurin yaduwa.

 

LEAVE A REPLY