Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i zai kaddamar da kyamarorin kan titi karo na farko a jihar Kadunaa ranar Juma’a. Za’a sanya na’u’rorin ne domin taimakawa jami’an tsaro gano masu aikata laifi a cikin birnin jihar a cewar hukumomi.

Mai taimakawa Gwamnan a harkar Sadarwa, Sa’idu Adamu ne ya bayyana hakan a jihar Kaduna.

“Wadannan Na’urori da za’a sanya akan tituna, zasu sanya ido sosai kan zirga zirgar jama’a, domin taimakawa jami’an tsaro gano tare da binciko masu laifi a babban birnin jihar” Adamu yana magana ne a lokacin da yake mayar da martani ga uwar jam’iyyar PDP ta kasa reshen jihar Kaduna.

Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta zargin Gwamnatin jihar da nuna halin ko in kula da al’amarin tsaro da yake neman tabarbarewa a babban birnin jihar.

Mista Adamu, yayi watsi da wannan zargi na uwar jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna, inda yace abin takaici ne da rashin kan gado.

“Gwamnatin jihar Kaduna na yin bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaro a dukkan fadin jihar Kaduna, abin takaici ne wani ko wasu su zargi wannan Gwamnati da gazawa ta fuskar tsaro a jihar”

“Gwamnati na kashe makudan kudade wajen sha’anin tsaro a jihar. A sabida haka, a ranar Juma’a 12 ga watan Janairu, Gwamna Nasiru el-Rufai zai kaddamar da na’urorin kantiti da zasu dinga taimakawa jami’an tsaro bibiyar masu laifi”

Gwamnatin jihar Kaduna ta ware kimanin Naira biliyan 2.55 domin samar da wadannan Na’urori domin taimakawa harkar tsaro a kasafin kudi na shekarar 2017.

Daga cikin wadancan kudade da aka ware, fiye da Naira biliyan 1.5 tuni an samar da wadannan kyamarori da su domin sanya su a gurare na musamman a cikin birnin jihar.

NAN

LEAVE A REPLY