Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasiru Ahmed el-Rufai taki amincewa da amfani da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwani na ‘Yan takarkaru a jihar Kaduna.

Wannan dai babban koma baya ne ga aniyar Sanata Shehu Sani na sake komawa majalisar dattawa a zaben shekarar 2019.

An jima da sanya zare tsakanin Gwamna el-Rufai da Sanata Shehu Sani, inda dangantaka tayi tsami sosai tsakaninsu.

Masu hasashe na ganin Gwamna el-Rufai ne ya fito da Malam Uba Sani takarar Sanata don ya kalubalanci Sanata Shehu Sani a zaben 2019 na majalisar dattawa na Kaduna ta tsakiya.

LEAVE A REPLY