Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sallamar malamai 4,562 cikin sabbin malaman da ta dauka aikin koyarwa kwanan nan bayan ta mika musu takardar barka da samun aiki.

Kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Ja’afaru Sani ya bayyana wanna a wani taron da ya halarta a jiya inda ya ce sabbin malaman 4,562 da aka kora sun samu shiga ne ta hanyar magudi ba don sun ci jarabawa ta biyu ba.

Ya ce, malaman basu cancanci su samu aikin koyarwa ba sakamakon kasa cin jarabawa na biyu ta gar da gar da jihar ta gudanar wa sabbin malaman da ta dauka.

Idan masu karatu dai basu manta ba, gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufa’i a watannin baya ta sallami malamai kusan 21,000 a jihar Kaduna sakamakon fadiwa jarabawan da suka yi na tabbatar da cewa sun cancanci koyar da kananan yara a makarantun firamare na gwamnatin jihar, da niyyar maye gurbinsu da wasu sabbin malamai 25,000

A yanzu haka kuma, a cikin sabbin malaman da jihar ta dauka, an yi tankade da rairaya inda aka sallami malamai 4,562  da suka kasa tsallake jarabawa na biyu, da cewa sun samu aikin ne ta hanyar magudi.

LEAVE A REPLY