Jagoran mabiya addinin Shiah na Najeriya,Ibrahim El-Zakzaky

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin jihar Kaduna ta maka hugaban kungiyar Shi’a ta ‘yan uwa musulmi, Ibrahim El-Zakzaky a kotu bisa zargin aikata laifuka 8 da a ciki har da aikata kisan kai.

Wannan ya biyo bayan zanga-zanga da ya yawaita daga mabiya El-Zakzaky a baya-bayan nan na kokarin tursasa gwamnati kan lalle sai ta saki shugaban nasu da ya samu tsawon lokaci a hannun gwamnati.

Lauyan El-Zakzaky, Femi Falana mai mukamin SAN ne ya bayyanawa jaridar Premium Times wannan batu a jiya Alhamis.

Falana ya ce, gwamnatin Kaduna na zargin El-Zakzaky da wasu sababbin laifuka 8, ciki har da kisan kai, wanda ke da hukuncin kisa.

Zarge-zargen sun biyo bayan karanbattan da ya wanzu tsakanin ‘yan kungiyar ‘yan uwan musulmi da tawagar hafsan sojin Nijeriya a Zaria a watan Disamban 2015.

Ko a makon da ya gabata ma dai sai da ‘yan Shi’a suka gudanar da zanga-zangar a saki El-Zakzaky da mai dakinsa da aka kama tun Disambar 2015. Zanga-zangar da ta haifar da dauki ba dadi tsakanin ‘yan shi’a da ‘yan sanda a Abuja.

LEAVE A REPLY