A kalla mutum 30 ake jin cewar ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace a jihar Borno a ranar Talata a kauyen Gamboru dake da iyaka da Jamhuriyar Kamaru.

Mutanen sun bar kauyen Wulgo dake kusa da Marte, kimanin kilomita 15 daga Marte din, sun tafi tare da adduna da amalanken katako domin debo itace da suka saro. Mutanen suna yin sana’ar ne domin samun abinda zasu rufawa kansu asiri.

Mutanen da aka sace din galibinsu matasa ne da ba su wuce shekaru 20 ba. Sun bar Gamboru ne akan iyakar Najeriya da Kamaru, yankin da ake jin mafakar ‘yan kungiyar ta Boko Haram ce.

 

Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya ruwato wannan labari.

LEAVE A REPLY