Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam

Gwamnatin jihar Yobe a ranar Alhamis ta bayar da tallafin motoci guda 20 samfurin Hilux wanda kudinsu ya kama Naira miliyan 350 ga rundunar sojan Najeriya.

Gwaman jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam shi ne ya hannanta mukullan motocin ga Shugaban hafsan tsoron Najeriya, Tukur Buratai a gidan Gwamnatin jihar dake Damatru.

Shugaban rundunar sojan kasa ta Najeriya, Tukur Buratai yana jihar Yobe ne domin duba yadda sojojin Najeriya dake aikin bayar da tsaro a jihar ke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewar, a yunkurin Gwamnatinsa na kyautatawa jami’an tsaron da ke jihar domin magance ayyukan ‘yan ta’adda, suka yi wannan kokari domin taimaka musu kawar da ‘yan kungiyar Boko Haram.

Haka kuma, Gwamna Geidam ya jaddada aniyarsa ta cigaba da taimakawa rundunar sojan Najeriya dake aikin bayar da tsaro a jiharsa, yace ya zuwa yanzu Gwamnatinsa ta baiwa sojojin dake jihar akalla motoci 300.

A lokacin da yake mayar da jawabi kan wannan tallafi, Tukur Buratai ya jinjinawa Gwamnatin jihar Yobe musamman akan yadda ta damu da batun tsaro da bayar da tallafi, a jihar da ma yankin Arewa maso yamma baki daya.

Lafatanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya kara da cewar, bayan tallafin motoci da gwamnatin jihar ke baiwa rundunar sojin, Gwamnatin kuma ta tallafawa da rundunar soja wani katafaren fili domin gina makarantar sojoji a garin Buni Yadi a jihar.

Haka kuma, kafin zuwansa gidan gwamnatin jihar Buratai ya gabatar da wata ziyara domin duba aikin gina asibitin sojoji a jihar da kuma duba sansanonin sojin Najeriya dake Damaturu a jihar.

NAN

LEAVE A REPLY