Gwamnatin jihar Legas ta haramta amfani da Amalanka da kura wadan da ‘yan dako ke amfani da su domin daukar kaya a cikin kasuwanni da tashoshin mota. Gwamnatin ta bayar da wannan sanarwa ne a ranar Asabar.
Sakataren Gwamnatin jihar Legas, Tunji Bello ne, shi ne ya bayyana haka.
Mista Bello, ya bayar da sanarwar ne inda yake cewar Gwamnatin tayi hakan da kyakkyawar niyya domin tsabtace jihar daga masu tura kura da suke bata lamura a jihar.

LEAVE A REPLY