Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu are da mai martaba Sarkin Yauri
Daga Shata Ne Auwal
Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen Abubakar Atiku Bagudu ne ya furta wadannan kalaman yau Lahadi a Fadar Maimartaba Sarkin Yauri, Bayan kammala ta’aziyyar rasuwar Alh. Ahmad Adamu Gungun Sarki Mahaifin Hon Aliyu Ahmad Adamu (DanIsan Yauri) Danmajalisar Dokokin Jihar Kebbi mai wakiltar Yauri a gidan Danmajalisar da ke Unguwar Gungun Sarki da kuma Fadar ga Maimartaba Sarkin Yauri Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi, CON. Da kuma ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su a wani Hatsarin jirgin ruwa da aka yi satin da ya gabata har ya yi Sanadiyyar mutuwar mutum 16 a karamar Hukumar mulki ta Shanga.
Gwamna Bagudu ya bada tabbacin gobe kwamishinan Ayukka na Jihar Kebbi zai zo tare da Injiniyoyin da za su yi aikin ba tare da bata lokaci ba. Gyaran dai zai fara ne daga Gadar Tondi/Gada zuwa Gadar Makirin (kan iyaka da Jihar Niger). Gwamnan ya ce gwamnatin Jihar Kebbi zata saka kudi a gyara Hanyar saboda samun saukin wahalar da mutane ke sha a hanyar.
Bayan haka Gwamnan ya bukaci Maimartaba sarki da ya bada wakili Wanda za a hada dashi zuwa Lagos Don sawo Jiragen Ruwan da zasu yi aiki kan kuwaran Wannan yankin (River Niger) saboda kauce ma yawan hadarurrukan da ake samu na ruwa, tare da bayyana kokarinsa da takwarorinsa Na Jihar Niger na neman izinin yankan itatuwan da ke cikin Rafukan a maikatar da ke kula da rafuka (NIWA) domin kauce wa samun hadurran jiragen ruwa.
Da yake jawabinsa, Maimartaba Sarkin Yauri Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi (CON), ya nuna Jin dadin sa kan ta’aziyyar da Gwamna ya kawo tare da neman Alfarma ga Maigirma Gwamna kan a gina karamar Cibiyar gidan Talabijin da Rediyon gwamnatin Jihar saboda ya Kai har Warrah a cikin karamar Hukumar mulki ta Ngaski.
Bayan haka Maigirma Gwamnan ya je tare da takwarorinsa gidan Alh. Umar Tambuwal daya daga cikin manyan Yan Siyasar yankin domin Gaida shi kan rashin Lafiyar da yake fama da ita.

LEAVE A REPLY