Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin jihar Binwai ta gurfanar da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a gaban kuliya a sakamakon ci gaba da kashe-kashen da Fulani makiyaya ke yi a jihar.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom, yayin da ya ke sanar da haka a yau jiya ya ce gwamnatin na tuhumar kungiyar da laifukan Kashe-kashe da tada zaune tsaye a kananan hukumoni 14 a cikin 23 da ke jihar.

Gwamna Ortom na magana ne a fadar gwamnatinsa da ke Makurdi a wani taron nanema labarai, inda ya ke bayyana matakan da gwamnatin sa ke dauka game da ci gaban kashe-kashen da jihar ke fuskanta.

Ya yi Allah wadai da rashin daukan mataki da hukumomin tsaro na jihar ke yi, lamarin da ya ce shi ya ta’azzara lamarin a cikin wannan shekara.

Idan mai karatu bai manta ba, gwamnatin Binwai ta aika takardar korafi ga gwamnatin tarayya da shugabancin hukumar ‘yan sanda da hukumar  ‘yan sandan farin kaya a shekarar 2017 game da barazanar da kungiyar Miyetti Allah ta yi wa jihar, tare da kiran a kama shugaban kungiyar, Abdullahi Badejo da sakatarensa, Alhassan Saleh.

LEAVE A REPLY