Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kashe zunzurutun kudi kimanin dalar Amurka biliyan 10 (Naira titiliyan 3.61) domin ayyukan raya kasa a cikin shekaru biyu kacal.

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki akan harkar zuba jari a Najeriya. Osinbajo ya ce an kashe kudaden ne galibi akan gina manyan hanyoyi da titin jirgin kasa da kuma batun samar da wutar lantarki.

Ya kara da cewar yana daga daga cikin abubuwan da wannan gwamnati ta baiwa muhimmanci shi ne sanya kudade masu yawa a harkar raya kasa da gine ginen manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.

 

LEAVE A REPLY