Wani sashe na butocin da Gwamnatin jihar Bauchi ta rabawa Masallatai a fadin jihar
Gwamnatin jihar Bauchi ta hannu Mai tallafawa Gwamnan Bauchi M A Abubakar akan kungiyoyin da bana Gwamnati ba da abokan kawo cigaba Alh Mansur Manu Soro ya bada sadakar butocin alwala har guda dubu goma (10,000) ga masallatai a fadin jihar Bauchi.
Mai tallafawa Gwamna ya mika butocin ga babban limamin masallacin Juma’a na Kofar Gombe kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Kwalejin Sharia da Musulunci dake Misau Sheikh Dr. zubairu Madaki domin rarrabasu ga masallatai.
Da yake karbar butocin, Sheikh Zubairu Madaki yayi addu’ar Allah Ya saka masa da alkhairi ya kuma yi alkawarin raba butocin ga masallatai daban-daban.

LEAVE A REPLY