Gwamnatin tarayya ta bayyana cewarzata rufe dukkan iyakokin Najeriya na kasa domin hana masu fasakwaurin shinkafa damar shigowa da ita daga kasashen da suke makwabtaka da Najeriya.

Ministan ayyukan gona da inganta karkara, Audu Ogbe ne ya bayyana hakan a Abuja ga manema labarai, a lokacin da yake jawabi gaban wata kungiyar matasa mai suna GOTNI.

Ogbe yace “daga cikin matsalolin da muke fuskanta a Najeriya bata wuce yadda kasashen makwabtanmu suke yi mana fasakwaurin shinkafa daga kasashensu ba”

“Irin yadda ake shigo da Shinkafa ta haramtacciyar hanya zuwa Najeriya ko Chana bata shigo manada kaya haka” A cewar Ministan ayyukan gona da inganta karkara Audu Ogbe.

LEAVE A REPLY