Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna ta bayyana cewar ta haramta dukkan wata zanga zanga a duk fadin jihar yayin da gobe Laraba ake sa ran gurfanar da Zakzaky a gaban kuliya.

Wannan jawabi ya fito ne a wata sanarwa da kakakin rundunar DSP Mukhtar Aliyu ya fitar inda yake bayyana cewar za’a jibge tarin jami’an tsaro a dukkan fadin jihar a gobe Laraba.

Sannan kuma ya shawarci mutanen jihar da su kasance cikin shiri tare da sanya idanu akan dukkan masu shige da fice a inda suke, musamman sanya ido akan wadan da aka ga motsinsu kuma ba’a sansu ba, a gaggauta kai rahoto zuwa ga caji ofis mafi kusa.

LEAVE A REPLY