Gwamnatin jihar Katsina ta ja hankalin matasa masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet akan zagi da cin zarafin manyan mutane a sabida bambancin ra’ayin siyasa ko wani abu mai kama da haka.

Kwamishinan Shariah kuma Attoni Janar na jihar, Ahmad El-Marzuq ne ya bayar da wannan gargadi a madadin Gwamnati a ranar Litinin a yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Daura.

Ya bayyana takaicinsa akan yadda tarbiyya take rushewa a shafukan sada zumunta na intanet,inda ake samun yara kananan na zagi da cin zarafin manyan mutane a dalilin bambancin ra’ayin siyasa a jihar.

A cewarsa, shafukan sada zumunta na intanet an kirkiro su ne domin hadaka cigaban al’umma da kawo sauye sauye masu ma’ana,amma abin takaici yanzu matasa sun mayar da su dandalin zin mutunci.

Mista Marzuq, wanda ya bayyana kalaman batancin da matasa suke yi a shafukan sada zumuntar kan iya janyo rashin fahimtar juna da rashin zaman lafiya tsakanin al’umma, wanda hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Ya bayyana cewar, tsarin Shariah na Najeriya ya tanaji hukunce hukunce akanduk wanda aka ci zarafi a wadannan shafuka, sannan yace, wadannan dokoki fa suna nan ba canza su aka yi ba, yana mai gargadi ga matasa da su kasance masu amfani da shafukan ta hanyoyin da suka dace don cigaban yankunansu da garuruwansu.

Kwamishinan, wanda ya bayyana tsarin shariah na jihar Katsina a matsayin “Mai cin gashin kansa” wanda yake aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kai tsakanin sassan Gwamnati guda uku domin cigaban jihar.

Yace, Gwamnatin Aminu Bello Masari ba zata zura idanu ta bar mutane na yin tabargaza da cin zarafin jama’a a shafukan sada zumunta na Intanet ba, yace dole ne mutane su nuna da’a da nuna mutunci da girmama na gaba.

Mista Marzuq, daga nan yayi kira ga al’ummar jihar Katsina da su cigaba da baiwa gwamnatin AMinu Bello Masari goyon baya a irin ayyukan da take yi na cigaban al’ummar jihar ba tare da wani nuna bambancin siyasa ko bangaranci ba.

 

NAN

LEAVE A REPLY