Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar a ranar litinin ya bayar da umarnin yin garambawul ga majalisar zartarwa jihar, inda aka canjawa kwamishinoni 9 ma’aikatu.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Shinkafi ya bayar, yace garambawul din da aka yi, ya haifar da gibi a wasu ma’aikatun, kamar ma’aikatar kananan hukumomi inda Kwamishina a ma’aikatar Muttaka Rini wanda aka mayar da shi ma’aikatar Ilimi.

Sanarwar ta acigaba da cewar, Lawal Liman, wanda ke ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma ya koma ma’aikatar lafiya, yayinda Mukhtar Lugga ya koma ma’aikatar Muhalli daga ta Ilimi.

SHaru Anka an mayar da shi ma’aikatar kasa da safiyo zuwa ma’aikatar gidaje da tsara birane, sai kuma, Sanda Dandari wanda a da shi ne Kakakin Gwamnati a matsayin kwamishinan yada labarai, inda yanzu ya koma ma’aikatar Albarkatun ruwa, yayinda Umar Jibona ma’aikatar shi kumaa ya koma yada labarai.

Sauran su ne, Suleman Gummi, wanda aka dauke daga ma’aikatar Lafiya zuwa ma’aikatar kasa da safiya, yayinda shi kuma Idris Keta wanda a baya shi ne kwamishinan ma’aikatar Kimiyya da fasaha yanzu ya koma ma’aikatar Raya karkara da cigabana al’umma, sai kuma Abubakar Ahmad da aka mayar ma’aikatar ciniki daga Kimiyya da fasaha.

Sanarwar ta kara da cewar, an tura sunan Dankande Gamji zauren majalisar dokokin jihar domin tantance shi a matsayin Kwamishina. Haka kuma, ana sa ran, majalisar dokokin jihar zata katse hutun da take yi domin tantance sabon kwamishinan da aka tura mata sunansa.

A ranar litinin din ‘yan majalisar dokokin jihar, sun zauna domin tattauna bukatar ta Gwamnan da ya aike musu. Dankande Gamji shi  ne Shugaban karamar hukumar Bakura, kuma shi ne Shugaban shugabanni na majalisar kananan hukumomin jihar Zamfara gaba daya da aka fi sani da ALGON.

NAN

LEAVE A REPLY