Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar

Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari ABubakar ya kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 500 wajen gyaran fadar mai martaba sarkin Gusau. Gwamnan ya kai ziyara fadar Sarkin ne domin duba yadda aikin gyaran fadar ke tafiya.

Haka kuma, Gwamnan ya kai ziyara domin duba sake aikin ginin hanyar Gusau Bypass me tsawon kilomita 23.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, Nan ya ruwaito cewar, Gwamnatin jihar Zamfara a watan Yulin da ya gabata ya baiwa kamfanin TRIACTA kwangilar ginin hanyoyi na kusan naira biliyan 2.2.

Gwamna Yari,wanda ya bayyana gamsuwarsa da ingancin ayyukan da ya duba, ya kuma bukaci dan kwangilar da yayi kokarin kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.

“Wannan gwamnatin tamu, tun farkon zuwanta, mun maida hankali kan ayyukan cigaban al’umma, wanda zasu taimakawa rayuwar al’umma” Gwamna Yari ya fada ta hannun mai taimaka masa wajen hulda da ‘yan jaridu, Malam Ibrahim Dosara.

Tun farko dai, Gwamnan ya gana da manyan masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro, domin tattauna al’amuran tsaron jihar, Gwamnan ya kuma, bukaci jama’a da su taimakawa gwamnati wajen bayar da kariya kan ayyukan da take yi domin cigaban al’umma.

A lokacin da yake nasa jawabin, Shugaban hukumar kula da kuma sanya ido kan ayyukan gwamnatin, ya tabbatarwa da Gwamna Yari cewar zasu tabbatar ‘yan kwangilar suna yin aikinsu cikin inganci da nagarta.

Haka kuma, kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewar, aikin sake ginin fadar Masarautar Gusau din da ake yi, shi ne irinsa na farko, na zamani da Gwamnatin take yi.

 

LEAVE A REPLY