Gwamnan jihar NejaAbubakar Sani Bello ya ja hankalin masu maganganu a shafukan sada zumunta na intanet da su guji yada kalaman batanci da kuma yada bayanan karya ko wadan da basuu tabbatar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun mai taimaka masa kan sabbin kafafen sadarwa na zamani, Yusuf Muawiyya a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kunciyar masu yada bayanai a sabbin shafukan sada zumunta na zamani.

Mai taaimakawa Gwamnan, ya ce “Irin maganganun da ‘yan Najeriya suke yadawa a shafukan sada zumunta na zamani domin kawo kiyayya da gaba bai dace ba”

Yayi kira ga matasan da su maida hankali wajen yada sahihan bayanai domin amfanin al’umma, da kuma watsa irin abubuwan cigaba a yankunansu wanda Gwamnatin jihar ta yi musu.

 

LEAVE A REPLY