Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu
Daga Shata Ne Auwal
Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagoracin Maigirma  Sen Abubakar Atiku Bagudu ta sake rubutawa Ma’aikatan Ayyukka ta Gwamnatin tarayya Takarda kan matsalar Hanyar da ta taso daga Jega-koko-yauri har zuwa Gadar Makirin, kan iyaka da Jihar Niger (Jega-koko-Yauri-Kontagora Road).
Image may contain: sky, tree, plant, cloud, outdoor, nature and water
A cikin takardar da ya sake aikawa,  Gwamna Bagudu ya yi Kira ga Gwamnatin tarayya da ta dauki mataki na Gaugawa kan Wannan Hanyar saboda mutanen yankin suna cikin mawuyacin Hali kan rashin kyawon hanyar.
Image may contain: one or more people and outdoor
Gwamnan ya furta wadannan kalaman ne Jiya Laraba 21/02/2018 a lokacin zaman Majalisar Zartarwar Jihar Wanda ya jagoranta a Dakin taron Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi.
Image may contain: one or more people, sky, cloud, outdoor and nature
Gwamna Bagudu ya ce ko satin da ya gabata ya ziyarci garin Yauri, kuma ya sake sanin yanayin Hanyar Hanyar ta da kyau ko kadan.

LEAVE A REPLY