Gwamnan Kaduna Nasiru el-Rufai

A wani taro da Gwamnan Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya halarta yau a Zaria yayin raba kayan tallafin karatu ga wasu dalibai. Gwamnan ya fashe da kuka ne a lokacin da yayi ido biyu da wani yaro da aka kwakwulewa ido kwanakin baya a Zaria.

Bayan da gwamna yaga wannan yaron ne ya tausaya masa matuka sannan, ya bukaci a kawo yaron kusa da shi ya zauna. Gwamna ya rungume yaron inda aka hango shi yana goge hawaye a idonsa.

LEAVE A REPLY