Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

Daga Yusuf Dingyadi

Gwamnan jahar Sokoto, Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal ya amince da rushe Majalisar Zartaswa ta jahar Sokoto wadda ta kunshi Kwamishinoninsa anan take.

Rushe Kwamishinonin ya biyo bayan bukatar da Gwamna Tambuwal yake da ita na sake tsara da nemo hanyoyin kwazo da ci gaban ayyukan raya kasa a jahar Sokoto anan gaba.

Bisa ga wannan a sanarwa da Darakta Janar na Watsa Labarai da Hulda da Yan jarida, Malam Abu Shekara ya sanya wa hannu ta nuna godiya ta mussaman daga mai girma gwamna ga dukkan Kwamishinonin dangane da irin namijin kokari da suka nuna tare da da’a, biyayya ga lamuran da suke da muhimmanci na ciyar jahar gaba.

Dangane da wannan Gwamnan Tambuwal yayi musu fatan alheri tare da bayar da umurnin hannunta dukkan ayyukan dake hannunsu ga manyan Sakatarorin ma’aikatun gwamnatin anan take.

Sanarwa daga
Yusuf Dingyadi
Babban Mataimaki na Mussaman ga Gwamna jahar Sokoto.

LEAVE A REPLY