Gwamnana jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal

Gwamnatin jihar Sakkwato a ranar Litinin ta bayyana cewar, ta rabawa injinan Taliya 3,500 ga mata domin yakar talauci da zaman banza a jihar a yunkurinta na rage radadin talauci ga al’ummar jihar.

Gwamnan jihar AMinu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka, a sanarwar da mai magana da yawunsa Imam Imam ya rabawa manema labarai a Sakkwato, inda ya kara da cewar, matan da suka amfana da wannan tallafi sun fito daga ko ina a fadin jihar.

A cewar Gwamnan, Gwamnatinsa na yin duk abinda zata iya wajen ganin ta yaki talauci da fatara a jihar, ta hanyar raba kayan dogaro da kai ga mata da matasa a dukkan fadin jihar.

Yace,jihar Sakkwato ta shahara wajen tallafawa mata da matasa wajen dogaro da kai a duk fadin Najeriya.

“Wannan tallafi yana zuwa ne, a lokacin da Gwamnati ta himmatu wajen taimakon raunana da masu karamin karfi, domin rage musu radadin talauci”

“Burin wannan Gwamnati ne ta samarwa da al’umma musamman matasa da mata hanyoyin dogaro da kai da kuma kananan sana’o’i domin mutane su dogara ga kansu”

“Irin wannan al’amari shi ne abinda Gwamnati ta sanya a gaba tun bayan zuwanta kan karagar Mulki shekaru biyu da suka gabata” A cewar Gwamna Tambuwal

Haka kuma, Gwamnan ya kara da cewar, Gwamnatinsa zata samar da dubban kekunan dinki da inin saka da baburan Adaidaita sahu domin rabawa a dukkan kananan hukumomin jihar 23.

NAN

LEAVE A REPLY