Daga Aji Kima Hadejia

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya jajantawa al’umar da ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a sassa daban daban na Jihar Jigawa, inda ya tabbatarwa waɗanda ibtila’in ya shafa samun tallafin gwamnati da kuma shirin gwamnatin na ɗaukar ƙwararan matakai don kawar da afkuwar irin wannan ibtila’i nan gaba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar duba yankunan da wannan ambaliyar ta shafa a Ƙananan Hukumomin Gumel, Kafin Hausa, Gumel, Ringim da Sule Tankarkar.

Gwamna Badaru wanda ya ziyarci yankunan tare da jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar Jigawa (JISEMA) domin duba irin ɓarnar da ambaliyar ya haifar, tare da tabbatar musu da cewa zai nemi Gwamnatin Tarayya ta shigo don tallafawa waɗanda abun ya shafa.

A yayin ziyarar, Maigirma Gwamnan ya umarci jami’an JISEMA da su fara raba kayan tallafi ga mutanen yankunan da wannan ibtila’i ya shafa.

Bayan ziyarar, Gwamna Badaru ya kai gaisuwar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II a fadar sa dake garin Gumel.

Gwamnan ya samu rakiyar wasu Kwamishinoni, masu riƙe da muƙamai da kuma Jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar Jigawa (JISEMA).

 

LEAVE A REPLY