Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar juma’a ya jagoranci kona wasu jabun magunguna da kimarsu ta kai kusan naira biliyan daya a cikin birnin Kano.

Gwamna Ganduje yace, wannan na daga cikin irin tanadin Gwamnatinsa na yaki da miyagun kwayoyi domin ceton rayuwar jama’a.

Gwamnan ya kara da cewar, Gwamnatinsa ta sake aikin fadada hukumar da take kula da wadan da suka kamu da shan miyagun kwayoyi.

Sannan Gwamnana ya bukaci kungiyoyi da al’umma da su taimakawa yunkurin Gwamnati na yaki da miyagun kwayoyi.

 

LEAVE A REPLY