Gwamnan Binuwai Samuel Ortom

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi Allah wadai da kakkausar murya bisa kisan da aka yi wa wasu fasinjojin motar haya a kusa da Yelwata da ke kan hanyar Lafia zuwa Makudi a jiya Asabar.

Majiyarmu ta gano cewa wasu wasu ‘yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba suka tare fasinjoji a kan hanyarsu ta tafiya suka kuma kashe mutum 3 daga fasinjojin.

Gwamna Ortom, a sanarwar da ya fitar ta bakin babban sakatarensa na yada labarai, Terver Akase, ya yabawa ‘yan sanda bisa gaggawar da suka yi na cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi don a yi musu hukunci daidai da laifinsu.

Gwamna Ortom ya yi kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da yin bincike don gano dukkan mutanen da ke da hannu a cikin wannan aika-aika.

Gwamna Ortom ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu, tare kuma da jan hankalin al’ummar jihar Binuwai da su ci gaba da zama masu bin doka da oda.

LEAVE A REPLY