Yusuf Dingyadi

Gwamnan jihar Sakkwato ya nada Alhaji Yusuf Dingyadi tare da wasu mutum hudu a matsayin mataimakana musamman.

Gwamnan ya bayar da sanarwar nadin nasu ne a ranar Litinin. Yusuf Dingyadi tsohon ma’aikacin gdan radiyon BBC Hausa kuma tsohon daraktan yada labarai na tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa.

Kafin nadin nasa dai, Yusuf Dingyadi ya rike mukamin Sakataren yada labarai na jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, inda daga bisani yayi murabus daga mukamin nasa.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta nuna cewar Alhaji Yusuf Dingyadi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin jihar, sai dai ana tarade radin cewar Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal na daga cikin Gwamnonin da ake jin cewar zasu balle daga jam’iyyar karkashin kungiyarsu tsa tsaffin ‘yan sabuwar PDP.

LEAVE A REPLY