Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, a ranar talata ya bayyana dalilan da suka sanya ya zabi sirikinsa a matsayin wanda zai gajeshi a kujerar Gwamnan jihar Imo da za’a nan gaba.

Gwamnan a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a filin sauka da tashin jirage na Sam Mbakwe dake birnin Owerri,jim kadan bayan dawowarsa daga kasar waje, Mista Okorocha ya bayyana cewar, sirikin nasa Mista nwosu ya cancanci ya gaje shi a matsayin Gwamnan Imo.

Ya tabbatarwa da al’ummar jihar cewar, za’a yi zaben fitar da gwani cikin gaskiya da adalci a jam’iyyar APC a jihar Imo. Babu wata karfa karfa ko kama karya wajen zaben dan takara.

Masu aiko da bayanai sun ce tuni ‘yan siyasa da dama a jihar suke ta sukar Gwamnan akan zaben sirikinsa da yayi a matsayin wanda zai gaje shi, suna fadinai mulkin ba gado bane ace ya dauko nasa yace sai shi.

Mista Okorocha ya kuma bayyana cewar, zaben kananan hukumomi a jihar ta Imo yana nan za’a gudanar da shi a watan Yuni na wannan shekarar, domin baiwa al’ummar jihar damar zaben wadan da zasu shugabance su a mataki na kananan hukumomi.

Ya kara da cewar yana yin duk mai yuwuwa wajen ganin ya tallata jam’iyyar APC kuma ta kai labari bama a jihar ba, har da dukkan jihohin yankin kudu maso yamma na Inyamurai, domin ganin mutanan sun karbi APC a zaben da ke tafe.

Gwamnan ya kara da cewar, zai yi kokari wajen ganin ya tallata Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yankin wajen ganin an kuma zabarsa a zaben 2019 dake tafe nan gaba a shekara mai zuwa.

NAN

LEAVE A REPLY