Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano za ta maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu in har ya ki ya amsa kiraye-kirayen da al’umma ta ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

Ganduje ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

“Gwamnonin APC na so Buhari ya zarce. Ina matukar murna kasancewar ba shi Buharin ne ya nemi da ya zarce ba don radin kansa, al’umma ce ta ke neman da ya zarce, kodayake dai har yanzu bai bayyana ra’ayinsa na zarcewan ba.”

“Na fada masa a lokacin da ya zo Kano, in har ya ki ya amincewa da ya tsaya takara a 2019, to lalle gwamnatin jihar za ta gurfanar da shi a gaban kuliya. A saboda haka muna sauraren jin ra’ayinsa,” inji Ganduje

“A kasar nan mun ga wani shugaban kasa da ya yi ta kashe biliyoyin Naira kawai don ya samu hawa na uku, saboda haka mene ne laifi ga wanda zai nemi hawa na biyu wanda dokar kasa ta sahale masa.”

LEAVE A REPLY