Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu

Kwamishinan ayyukan gona na jihar Kebbi, Garba Dandiga ya bayyana cewar, Gwamnatin jihar ta shirya tsaf domin rabawa manoma tarakta guda 300 da kuma injinan yankan shinkafa guda 250 domin bunkasa noman Shinkafa a jihar.

Dandiga ya bayyana haka ne a ranar Talata bayan da ya jagoranci wata tawaga zuwa gonakin Shinkafa dake Kamba da Jega da Suru a yankunan kananan hukumomin Jega da Suru.

Ya kuma kara da cewar, fiye da kilo mita 70 na gonakin shinkafa ne aka nome su a jihar.

kwamishinan ya cigaba da cewa, gwamnatin kuma zata raba sauran kayayyakin aikin gona ga manoman akan farashi mai rahusa domin bunkasa aikin noman Shinkafa a jihar.

“Tuni Gwamnatin jihar ta fara yin feshin maganin kwari a gonakin shinkafa na jihar, domin rigakafi ga tsuntsaye da kwari masu lalata amfani”

“Gwamnatin na yin wannan feshi ne domin kaucewa asarar abinda aka shuka”

Ya ce, ana sa ran samun fiye da tan miliyan biyu na shinkafa daga manoman jihar a wannan shekarar ta 2018.

“A shekarar da ta gabata, jihar Kebbi ta samar da tan miliyan guda na shinkafa”

“A saboda haka, wannan shekarar muna sa ran samun tan miliyan biyu na shinkafa, saboda manoma da yawa sun shiga harkar noman Shinkafa sosai da sosai” A cewar kwamishinan.

Kwamishinan, har ila yau, ya kara da cewar, kananan hukumomin jihar 15 sun mayar da hankali sosai akan abinda ya shafi noman shinkafa.

NAN

LEAVE A REPLY