Gwamnatin jihar Sakkwato ta raba jiragen ruwa 22 domin bunkasa harkar sufuri a ruwa, kamar yadda Gwamnatin ta bayyana.

Babban darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA, Ibrahim Dingyadi ne ya bayyana hakan a jihar Sakkwato, ya kuma kara da cewa, Gwamnatin ta yi hakn ne domin samar da aminci a harkar sufuri da ake yi a kwale kwale.

“Yana daga cikin kudure kuduren Gwamnatin Sakkwato ta yanzu, tayi kokarin ta magance aukuwar bala’o’i da kuma kokarin kiyaye rayuwar al’umma daga fadawa garari”

“Ana yawan samun hadarin jirgin ruwa yankunan Sakkwato da suke da ruwa, ko asamu nutsewar kwale kwale, shekarar da ta gabata an samu irin wannan hadari a kauyen Gandi dake karamar hukumar Rabah,inda wata yarinya ta rasa ranta, a lokacin da ‘yan kasuwa ke tafiya kasuwanci”

“A dan haka ne, Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana kawo karshen irin wadannan matsaloli ta hanyar samar da sabbin jirage 22, kuma aka rarrabasu zuwa ga yankunan da suke da ruwa domin yn sufuri”

“An yi hakan ne domin kare sake aukuwar irin wadannan hadarurruka anan gaba, tare da kokari kare rayukan al’umma, wanda kuma mutanan da akaiwa abin sun nuna jin dadin da kuma gamsuwarsu”

Jirage guda takwas an tura su zuwa Goronyo, yayin da aka tura hudu Silame sannan kuma aka baiwa Rabah guda goma.

Babban daraktan hukumar SEMA yace tuni hukumarsu ta shiga aikin wayar da kan mutane tare da nuna musu illar yin abubuwan da kan janyo hadarin ruwa a jihar.

Mista Dingyadi yaciga da cewar, a shekarar da ta gabata, gwamnatin Sakkwato ta kafa wani kwamiti da zai duba hanyoyin magance irin wadannan bala’o’i da kan faru, kwamitin da mataimakin Gwamna Ahmed Aliyu yake shugabanta.

Ya cigaba da cewa, Kwamitin yayi kokarin wajen ganin an ilimantar da mutane irin hadarurrukan dake tattare da kauce tsari, inda Kwamitin ya dauki hayar mutane 550 domin wayar da kan mutane kan yadda zasu kula da muhallinsu.

Daraktan ya kara da cewar, hukumarsu tana aiki da kafada da kafada da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma Red Cross da Malaman addini da kungiyoyi masu zaman kansu da ba na Gwamnati ba wajen ganin an wayar da kan al’umma.

Daga karshe Daraktan ya bukaci, al’umma da su taimakawa yunkurin Gwamnati na magance irin annobar da kan samu muhalli, tare da kai rahoton dukkan wani abu da aka san zai haifar da bala’i domin magance shi cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY