Tsohon Gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu

An gurfanar dan tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu mai suna Nuraini Adamu da shi da wani mai suna Felix Onyago a wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a jihar Kano a jiya Laraba bisa laifin safarar kudade da adadinsu ya kai Naira miliyan 32.

Furosikwuitan kotun, Douglas Gift ya shaidawa kotun da mai Shari’a Daggard ke jagorantar sauraron shari’ar cewa wadanda ake karar biyu sun hada kai wajen aikata laifin da ake zarginsu da shi ne a shekarar 2014.

Mista Gift ya ci gaba da bayyanawa kotu cewa, Nuraini ya tura kudade ga Felix Naira miliyan 32 duk a cikin shekara guda. Wannan ya sabawa sashen doka na 18(a) da sashe na 15 da sashe na 2 (b) na dokar safarar kudi na Nijeriya.

Mai Shari’a Daggard a yayin da ya ke yanke hukunci kan batun bayar da belin wadanda ake zargin biyu ya bayyana cewa sai sun kawo mutum biyu da za su tsaya musu. Ya kara da cewa dole daya daga cikin mutanen da za su tsaya musu din ya zama mazaunin Kano.

Mutum na biyu kuma dole sai ya zam dan uwa na jini ga wadanda ake zargin kuma ya kasance yana da kadarar da ta danganci fuloti wanda dole zai bari a hannun kotun.

Wadanda ake zargin dai basu amsa laifukansu ba, a saboda haka an bayar da belinsu tare da daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga Maris, 2018.

LEAVE A REPLY