Ranar Asabar din da ta gabata aka yi zabe a jihar Kano, zaben da yake cike da kura-kurai da rudani. Hasalima, Kano bata taba ganin lalataccen zabe irin wanda aka gabatar a ranar ba. Hakika, bai ma kamata mu kira shi zabe ba. An dai debi kudaden talakawa, wadanda aka matse, aka takura da sunan haraji, aka zo kuma aka lalata dukiyar, a wannan shiriritar da aka yiwa lakabi da zabe. Wannan zaben shi ya kara tabbatarwa da al’umma cewar Gwamnan Kano Ganduje, ya gaza ta ko wace fiska.

Tunda fari, komai da ya danganci zaben a hagun ce aka yi shi, da badakala, da kumbiya- kumbiya. Misali an ki a saidawa jama’a form din takara, sai fa ‘yan gandujiyya, kurum don a basu dama, a dakile wadansu. Akwai hujjoji kwarara.

1- An bayar da nambobin account har 3, wanda a fadar su, sune account din da za’a saka kudin siyen form. Hakan ya kawo rudani, domin mutane da dama da suke son siyen form din takarar, sun kidime, basu san wanne ne sahihin account din da zasu saka kidin siyen form ba, don suna tsoron su saka a account din bogi. Shin a ina kuka taba jin an bada mabanbantan account number a sayi form din takara? Na tabbata anyi hakan ne don mutane su shiga eudani. Yasu- yasu, sun san account din gaskiyar.

2- Wannan dama wasu dalilai, suna daga cikin dalilan da yasa mutane basu dita zaben ba. Bugu da kari, jama’ar jihar Kano, kuma yan jam’iyyar APC mafibyawan su, ‘yan Kwankwasiyya ne. Son haka ba abin mamaki ne ba, suki fita zaben, domin dai an riga an bada umarni cewar kada yan Kwankwasiyya su fita zaben. Da yake mune da Jama’ar, sai filin zabukan suka zama fayau- sai tsirarun mutane

Wai kuma duk wannan bai ishi gwamnati izina ba, idanun ta ya rufe- so kawai ake ace an ci zabe. Don haka ta ci gaba da shirin ta. Shirin da shi kansa ya nuna gazawar ta. Domin a mafi yawan mazabun, ba’a kai kayan aikin zaben ba sai bayan azahar, wasu ma kusan la’asar, kuma wai kafin karfe hiyar na yamma an gama zabukan.

Ba mamaki hakan ta iya faruwa, don a zahiri, ba mutanen. Sannan babban kuskuren da gwamnati ta tafka shine, kananun yara da suka debo, wadand shekarun su bai kai zabe ba, ta jera su a layi suka yi zaben, wai kawai kada ace ba’a yi ba. inda basu samu yaran ba kuma, ma’aikatan zaben suka dangwale takardun zaben da hannun su. Wannan abin kaico ya isa. Kuma wannan ba fada ta bace, kusan duk gidajen rediyo sun rawaito zaben a halin da ake gudanar da shi. Abin dai sai gyaran Allah. Abin takaici, Gwamna da kansa da yake zabe bai ji da dadi ba- a mazabar gwamna, a gaban idon sa aka dinga yi masa ihun “ba ma yi… yunwa.. ” da makamantan wannan kalaman. Allah ya sakawa ‘yan jaridar mu da alheri. Ba don su ba, da an ninke mu bai-bai.

Don haka, ina jan hankalin gwamnati ta lura cewar wannan zaben ba abin da ya kara mata sai batanci. Ta fado kasa wanwar- dole jama’a su ga wallen ta.

Sannan ina jan hankalin al’umar gari da mu dage, kada mu yarda a dinga amfani da ‘ya’yan mu, ana tsoma su a harkokin siyasa alhalin shekarun su ma ba su kai ba.

Duk wanda ya yarda da ni ya daga hannun sa sama yace “aye”

 

LEAVE A REPLY