A kalla mutane 3 ne suka mutu yayin da aka yi asarar gidajen da kimarsu ta kai naira miliyan 50 a wata guguwa mai karfin gaske da ta tashi a yankin Duguri dake yankin karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Babban darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi SEMA, Yusuf Kobi ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin labarai na Najeriya, NAN, faruwar wannan al’amari a yankin karamar hukumar alkaleri.

Yusuf Kobi yace garuruwan da wannan guguwa ta shafa sun hada da Yuli da Bandibitda Gaji da Bun da Bayak da Kunzum da Tummi da Nyalan da Tonlon da Bajoga da Taksamat da a yankin gundumar Yali.

Sauran su ne Sharan da Dugudi a yankin gundumar Dun.

LEAVE A REPLY