Ministan kulada albarkatun ruwa, Sulaiman Adamu, a ranar Alhamis ya koka kan yadda Madatsar ruwa ta Goronyo dake jihar Sakkwato ke barazanar kafewa.

Mininstan wanda ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ababban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewar yana daga cikin irin illar da sauyin yanayi ya haifar ga rayuwar al’umma shi ne na samun irin wannan kafewa.

Ya kara da cewar, tuni ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasa ta himmatu wajen bin hanyoyin da take ganin ya dace abi wajen ceto wannan madatsar ruwa tun kusan shekaru biyu da suka gabata.

Asakamakon ziyararbazata da ma’aikatar ta kai a ‘yan kwanakin nan, ya nuna akwai bukatar gaggawa wajen ganin an dauka dan kaucewa abinda ke neman faruwa da wannan madatsar ruwa.

“Na kadu sosai akan halin da naga wannan madaatsar ruwa, idan zaku iya tunawa, a shekaru biyu da suka gabata, na halarci wajen wannan madatsar ruwa, domin duba adadin yawan ruwan da ya rage”

“Amma sake ganin abin da na yi bayan shekara biyu abin yayi matukar tsoratani kwarai da gaske”

“Babu ko shakka, wannan shi ne abinda ake kira sauyin yanayi wanda muka gani da idanunmu, kai wannan fa tabbas ne”

Ya bayyana cewar madatsar ruwa ta Goronyo, wanda ita ce madatsa ta biyu mafi girma a duniya, wadda take a Arewacin Najeriya, an gina ta da nufin ajiye ruwan da ya kai kubin mita biliyan daya, amma yanzu ta bushe bai wuce kashi 10 ne na adadin ruwan kadai ya rage ba.

“Bamu taba yin tsammanin haka ba, a irin wannan karafariyar madatsar ruwa, amma kuma gashi hakan ta faru, wannan yana nuna cewarmuna da gagarumar matsala a gabanmu”

 

LEAVE A REPLY