Tsohon Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya samu sabon mukamin shugaban wata hadaddiyar runduna da zata sanya ido a zaben kasar Saliyo, wanda za’a gudanar a ranar 7 ga watan maris na wannan shekarar ta 2018.

Goodluck Jonathan zai kasance a matsayin jagora masu sanya ido na hukumar tarayyar Afurka mai suna EISA.

A ranar Juma’a ne ake sa ran tsohon Shugaban kasar zai bar Najeriya zuwa birnin Freetown.

Wannan bayani na zuwa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon Shugaban Ikechukwu Eze shi ne ya bayyana hakan.

Mista Eze ya bayyana cewar, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna gamsuwarsa da samun wannan sabon mukami, a kokarinsa na ganin anyi zabe lami lafiya a nahiyar Afurka.

 

LEAVE A REPLY