Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa tana da takardun da ke bayyana yadda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayar da umarnin cire sama da Naira Biliyan 100  daga babban bankin Nijeriya, CBN aka kai masa gida don rabawa ‘yan siyasa, makonni biyu kafin zaben 2015.

Tun da farko dai, Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osibanjo ya nuna cewa wadannan kudade da aka zara daga CBN sun yi matukar girgiza tattalin arzikin Nijeriya, inda ya nuna cewa har yanzu tattalin arzikin kasar nan na fama da masassara ne sakamakon wannan diban karar mahaukaciya da gwamnatin Goodluck ta yi wa asusun Nijeriya.

LEAVE A REPLY