Daga Hassan AbdulMalik

Wata gobara da ta tashi cikin a kasuwar ‘Yan katako da ke a Rijiyar Lemo, Kano ta lankwame shaguna 22 a daren jiya Talata zuwa asubuhin yau Laraba.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Sa’idu Muhammad ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 3:10 na dare.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 3:10 na dare daga wani Muhammad Yahaya daga unguwar Kurnan Asabe, inda ya sanar da mu cewa wuta ta tashi a kasuwar ‘yan katako,” inji Alhaji Sa’idu, kakakin hukumar kashe gobara.

“da samun wannan labari ne sai muka tura jami’anmu zuwa kasuwar kuma sun isa wajen gobarar da misalin 3:14 dauke da kayan aikin kashe gobarar.”

Kakakin ya ci gaba da cewa har zuwa wannan lokaci ba su tantance abinda ya yi sanadiyyar tashin gobarar ba, amma suna kan yi binciken dalilin.

Kakakin ya yi kira ga ‘yan kasuwar da su kara kulawa wajen yadda suke yin amfani da na’urorin masu aiki da wutar lantarki da don kaucewa faruwar hadarin gobara.

Ya kuma da kara da cewa, ya kamata kowane dan kasuwa ya mallaki kayan kashe gobara a shagonsa, ta yadda za a iya magance karamar gobara da zarar ta tashi ba har sai ta girmama ta fi karfin mutane ba ta yadda dole sai an kira jami’an kashe gobara ba, wanda watakila kafin su zo watakila an tafka asara.

LEAVE A REPLY