Daga Hassan Y.A. Malik

A cikin jami’an ‘yan sanda guda 371,800 da ake da su a Nijeriya, an gano cewa kimanin 80,115 na bogi ne.

Wannan ya na kunshe ne a wani bayanai da jaridar Premium Times ta samo daga ofishin akawunta janar na Nijeriya.

Bayanan sun nuna yadda aka gano wannan badakala bayan da aka fara amfani da sabon tsarin biyan albashi na gwamnati tarayya (IPPIS), inda aka hada bayanan jami’an reshina 42 na rundunar ‘yan sandan kasar.

Adadin ma’aikatan da aka shigar tsarin shine 291,685 wadanda a hade ke karbar albashin kimanin Naira biliyan 22.3

Wadannan jami’an bogi da manyan ofisoshin rundunar suka kasa bayani akan su sun shafe shekaru suna tasar Nijeriya biliyoyin nairori.

A yayin taron majalisar zartarwa na makon da ya gabata ne ministar kudi ta Nijeriya, Kemi Adeosun ta gabatar da sabon rahotan kaddamar da sauyin zuwa tsarin IPPIS.

Ministar ta ce ma’aikatu 511, bangarorin gwamnati da hukumomi sun shiga sabon tsarin da ma’aikata kimanin 607,843.

LEAVE A REPLY