Gwanan kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya shiga tsakanin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano dake yunkurin tsige kakakin Majalisar Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata bisa wasu zarge zarge da suke yi masa.

Tun a jiya dai kimanin ‘yan majalisa 24 ne suka sanya hannu akan takardar tsige Kakakin majalisar, abinda ya nuna goyon bayan ‘yan majalisa 3 kacal ake nema wajen kwabe rawanin Kakakin majalisar Abdullahi Ata.

Sai dai kuma, bayan da lamura suka rincabe, Gwamnan jiharGanduje ya shiga tsakaninsu inda aka jingine batun tsige Kakakin majalisar ya zuwa yanzu.

Ko meye ra’ayinku kan wannan batu?

LEAVE A REPLY