Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na shirin nada kwamishinan gona na jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sabon mataimakinsa.

Kujerar mataimakin Gwamnan Kano ta zama ba kowa tun bayan murabus din Farfesa Hafizu Abubakar da yayi.

An jima ana rade radin mutumin da Ganduje zai dauka a matsayin mataimakinsa. Anyi ya kawo sunaye da yawa na mutanan da ake ganin Ganduje zai zaba a matsayin sabon mataimakinsa.

Sai dai yanzu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewar Gwamna Ganduje na shirin baiwa Nasiru Gawuna kujerar mataimakin Gwamna.

LEAVE A REPLY