Hukumar kula da gidajen yari ta jihar Legas ta bayyana cewar akalla fursunoni 35 a kurkuku dake Ikoyi suka rubuta jawarabar karshe ta kammala Sakandire ta SSCE wadda ake yi a tsakanin watannin Janairu/Fabarairu.

Kwanturolan fursunoni na jihar Legas, Tunde Ladipo ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN a Legas ranar lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito ewar wannan wata sabuwar jarabawa ce da hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afurka WEAC ta bullo da ita. Ana gudanar da jarabawar ne a manyan birane da garuruwa kawai.

Mista Tunde yace, hukumar kula da gidajen yari ta jihar Legas na aiki tukuru wajen ganin an baiwa daurarru daman samun ilimin boko a gidajen kurkuku.

“Ina mai farincikin sanar da ku cewar, walwalar wadannan ‘yan kurkuku na daga cikin abinda muka baiwa muhimmanci”

“Muna yin dukkan bakin kokarinmu wajen ganin mun kyautatawa daurarru domin samun walwala da jin dadi a yayin da suke zaman wakafi, tare da tabbatar da cewar suna samun abinda ya kama su ci gajiyarsa a matsayinsu na daurarrau”

NAN

 

LEAVE A REPLY