Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello

Daga Hassan AbdulMalik

Kimanin mutane 32 ne suka rasa rayukan su a wani sabon rikici da ya barke tsakanin Fulani makiya da manoma a garuruwan Dekina da Omala a jahar Kogi.

Rahotanni daga jaridar The guardian sun bayyana yadda makiyayan suka isa garuruwan ta kwale kwale a ranar Larabar da ta gabata, inda suka bude wuta akan mutane tare da kona gidajen su. Wani ganau ya fadawa jaridar cewa sun isa ne sanye da kayan sojoji kuma dauke da bindigun AK47.

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai su 500 kuma sun kona gidaje sama da 20 tare da harbe duk wanda suka gani, a ciki har da wadanda ke yunkurin guduwa.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jahar, Monday Bala ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai a jiya Asabar, sai dai bai fadi adadin mutanen da suka rasu ba.

A cikin wadanda suka rasu, har da mutane hudu a cikin iyalin wani jami’in dan sanda, kamar yadda rahotan ya shaida.

A cewar wani magidanci a yankin, za ta iya yiwuwa harin na ramuwar gayya ne akan wani rikici da ya faru a yankin tun a 2016 inda aka kashe Fulani guda 4 da shanu da dama.

Idan mai karatu bai manta ba,  a watan Fabrilun shekarar nan ne gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello ya ware hekta 15,000 na filaye domin aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na samar da biranen makiyaya, inda gwamnan ya nemi Fulani makiyaya da su koma jahar da zama tunda sub a su da dokar hana kiwo kamar makociyar su jahar Benue.

LEAVE A REPLY