Hukumar lafiya a matakin frko ta jihar Jigawa, ta bayyana cewar fiye da yara miliyan daya da dubu dari shida (1.6m) ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar poliyo a jihar, a karon farko na farkon wannan shekarar ta 2018 a dukkan fadin jihar.

Babban sakataren gudanarwar hukumar,Kabiru Ibrahim ne ya bayyana haka a birnin Dutse a ranar alhamis.

Kabiru Ibrahim yace, shirye shirye sunyi nisa wajen samun adadin mutanan da zasu zaga cikin jihar domin yiwa yaran da ake sa ran yiwa allurar a wannan shekarar, a kananan hukumomin jihar 27, domin tabbatar da cewar dukkan yaran da ba su kai shekara biyar ba anyi musu wannan allurar a fadin jihar.

Ya kara da cewar, hukumar ta karbi isassun magungunan allurar samfurin OPVs, da kumaalkalamin shaidar wanda akaiwa daga hannun Gwamnatin tarayya domin samun nasarar wannan aiki.

Babban sakataren gudanarwar, yace ya zuwa yanzu babu wani shiri da bai kammala domin fara wannan allurar ba a duk fadin jihar.

Mista Ibrahim, ya nemi goyon bayan al’ummar jihar baki daya, musamman sarakunan gargajiya da malaman addini da Limamai da dukkan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar yin wannan allurar.

Sannan kuma, ya bukaci iyaye da su bayar da yaransu domin yi musu wannan allurar ta rigakafi, a dukkan wuraren da aka tsara za’a yi wannan allurar a dukkan unguwanni.

Ana sa ran za’a fara yin wannan allurar ne ta wannan shekarar a ranar 20 ga watan Janairun nan.

LEAVE A REPLY